Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Ko wane mataki kasashen duniya za su dauka kan Turkiya?

A wannan Larabar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai sake gudanar da zama don tattaunawa kan farmakin da dakarun Turkiya ke kaddamarwa a arewacin Syria, yayin da shugaban Turkiyar Racep Tayyip Erdogan ke cewa, ba su da niyar dakatar da wannan farmaki duk da matsin lambar da suke fuskanta daga kasashen duniya. Yanzu haka ana fargabar cewa, sakamakon wannan farmaki, akwai yiyuwar mayaka masu nasaba da kungiyar ISIS sun arce daga yankin.

Daya daga cikin wuraren da Turkiya ke lugudan wuta a Syria
Daya daga cikin wuraren da Turkiya ke lugudan wuta a Syria REUTERS/Stoyan Nenov
Talla

A daidai lokacin da farmakin na Turkiya ke ci gaba da haddasa cece-kuce a sassan duniya, kasar Amurka ta ce, ba ta da masaniya game da gagarumar tserewar mayakan ISIS daga fursunonin da dakarun Kurdawa ke tsare da su.

Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun ce, hare-haren Turkiyar sun yi sanadiyar tserewar ‘ya’yan kungiyar ta ISIS masu hadarin gaske.

A bangare guda, kasashen Birtaniya da Spain sun bi sahun manyan kasashen duniya wajen dakatar da sayar wa Turkiya makaman soji saboda wannan farmakin da take kaiwa.

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Dominic Raab ya ce, daga yanzu ba za su bayar da lasisin shigar da makamai cikin Turkiya ba wanda za a iya amfani da su a Syria, yayin da kasar Spain da ke kan gaba wajen sayar wa da Turkiyar makamai, ita ma ta sanar da daukar irin wannan mataki.

Sai dai Turkiyar ta yi watsi da matakin da kasashen duniya suka dauka na juya mata baya, tana mai cewa za ta ci gaba da aikinta na kakkabe duk wata kungiyar ‘yan ta’adda da suka hada da mayakan ISIS a Syria.

A bangare guda, shugaban Amurka Donald Trump ya ce, mataimakinsa Mike Pence da kuma Sakataren Harkokin Wajen Kasar, Mike Pompeo za su tashi zuwa Turkiya a wannan Laraba.

Trump ya shaida wa manema labarai a fadarsa da ke Washington cewa, zai yi kokarin samar da tsagaita wuta a farmakin na Turkiya, kuma saboda haka ne ya bayar da umurnin sanya wa kasar takunkumai.

Kazalika shugaban Rasha Vladimir Putin ya gayyaci Erdogan zuwa birnin Moscow domin tattaunawa dangane da wannan rikici.

Sanarwa da fadar Keremlin ta fitar a safiyar yau, ta ce, nan ba da jimawa ba ne Erdogan zai isa birnin na Moscow bayan da shugabannin biyu suka tattaunawa ta wayar tarho a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.