Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Turkiya ba za ta daina luguden wuta a Syria ba - Erdogan

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce kasar sa ba za ta dakatar da luguden wutar da take kan Kurdawa a arewa – maso gabashin Syria ba duk da sukar da ake yi, har sai ta samu nasarar da ta ke bukata.

Shugaban Turkiya Recep Dayyib Erdogan
Shugaban Turkiya Recep Dayyib Erdogan Murat Cetinmuhurdar/Presidential Press Office/Handout via REUTER
Talla

Shugaba Erdogan ya ce sun kudiri aniyar ci gaba da wannan yaki har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi, kuma za su yi biris da duk wata barazana har sai hakarsu ta cimma ruwa.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin wani jawabi a birnin Baku, inda ya caccaki Tarayyar Turai da kungiyar kasashen Larabawa masu sukar hare – haren da kasar sa ke kaiwa, yana mai neman su baiwa Turkiyya kudaden da suka alkawarta na shirin samar da tudun mun tsira a arewa maso – gabashin Syria.

A wani mataki na goyon baya, jakadan Turkiyya a Qatar, Fekret Ozer ya ce kasar za ta ci gaba da wannan diran mikiya da take yi a arewacin Syria har sai ta kawar da duk wata barazana ta’addanci a kan iyakarta da Syria.

A makon da ya gabata, Turkiyya ta kaddamar hare –hare ta sama da kasa kan Syria, inda ta ce ta yi hakan ne don kakabe dakarun Kurdawa daga yankin kan iyakan ta da Syria, sannan ta samar da tudun mun tsira da za ta sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar Syria.

Wannan mataki na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da shirin janye sojin Amurka daga yankin, wadanda kasancewarsu a wurin ta zama tamkar kariya ga ‘yan tawayen Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.