Isa ga babban shafi
Italiya

Masu ra'ayin rikau sun yanke kawance da gwamnatin Italiya

Ministan cikin gidan kasar Italiya mai tsatsauran ra’ayi Matteo Salvini, ya sanar da kawo karshen kawancen da ke tsakanin jam’iyyarsa da gwamnatin da ke kan karagar mulkin kasar, inda ya bukaci a shirya sabon zabe. To sai dai Firaminista Giuseppe Conte, ya ce ministan cikin gidan ba shi da hurumin kiran sabon zabe a karkashin dokokin kasar.

Matteo Salvini
Matteo Salvini REUTERS/Alessandro Garofalo
Talla

Shirya sabon zaben a cikin gaggawa da ministan cikin gida Matteo Salvivi ya bukaci a yi, abu ne da ya fito fili da sabanin da aka jima ana rade-radin cewa ya dabaibaye gwamnatin kawancen da ta share tsawon watanni 14 kan karagar mulkin kasar ta Italiya.

Duk da cewa akwai bambancin ra’ayi a fannoni da dama tsakanin jam’iyyun da suka kafa wannan kawance, to sai dai matsalar ta kara fitowa fili ne bayan da gwamnatin Firaminista Gueseppe Conte ta sanar da kulla kawancen gina layin dogo da zai hada birnin Lyon na Faransa da kuma Turin na Italiya cikin wannan mako.

Kafin wannan sabon rikici, dama an sha samun sabani tsakanin Salvini da kuma mataimakin firaminista Luigi di Maio a game da batutuwa da dama, da suka hada da siyasar karbar baki da kuma mutunta wasu ka’idoji na kungiyar Turai.

A cikin yanayi na ba-zata ne ministan cikin gidan ya sanar da janyewar jam’iyyarsa daga gwamnatin kawancen, inda ya bukaci a shirya sabon zabe a cikin gaggawa, to sai dai Firaminista Gueseppe Conte ya ce shugaban kasa kawai ne ke da hurumin kiran sabon zabe amma ba ministan cikin gida Salvini ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.