Isa ga babban shafi
Afrika-Italiya

AU ta bukaci Salvini ya janye kalaman kaskanci kan Afrika

Kungiyar Kasashen Afrika ta AU ta bukaci Ministan Cikin Gidan Italiya, Matteo Salvini da ya janye kalaman batancin da ya furta da ke bayyana ‘yan Afrika a matsayin bayi.

Matteo Salvini
Matteo Salvini REUTERS/Tony Gentile
Talla

Kungiyar ta nuna takaicinta da kalaman Ministan wanda ta bayyana a matsayin kaskanci ga mutanen nahiyar.

Sai dai Salvini ya hakikance cewa, an yi wa kalamansa mummunar fahimta kuma babu bukatar neman afuwa akai.

A ranar juma’ar da ta gabata, yayin mahawara kan bakin da ke zuwa Turai, Salvini ya ce, su a Italiya sun mayar da hankali wajen sanya jama’ar kasar kara haihuwa maimakon karbar wasu bayi, kalaman da ya harzuka mutane da dama.

Jim kadan da nada shi Ministan Cikin Gida, Salvini ya yi alkawarin rufe tashoshin jiragen ruwan Italiya don dakile kwararar bakin haure da masu neman mafaka a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.