Isa ga babban shafi
WHO-Lafiya

Hukumar lafiya ta duniya ta koka da yawaitar sukari a abincin Jarirai

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO, ta bayyana damuwa kan abinda ta kira yawan sikarin da kamfanonin dake sarrafa abincin jarirai ke laftawa, wadanda ke yiwa yaran illa.

Wasu nau'ikan abincin yara kanana
Wasu nau'ikan abincin yara kanana Zeenat Hansrod
Talla

Hukumar ta ce ta gudanar da bincike kan irin wadannan nau’yin abinci har 8,000 daga shaguna sama da 500 da ake sayar da su a kasashen Austria da Bulgaria da Israila da kuma Hungary tsakanin watan Nuwambar shekarar 2017 zuwa Janairun shekarar 2018, kuma sama da kashi 30 na irin wadannan abinci na dauke da zakin da ya wuce kima.

Hukumar ta WHO ta ce duk da ya ke kayan marmari na dauke da nauyin sikari a cikin su, yadda masu sarrafa kayan abincin ke kara sikarin na haifar da matsalar kibar da ta wuce kima da kuma lalacewar hakora.

Daraktan Hukumar a Turai, Zsuzana Jakab ta ce samun abinci mai inganci lokacin yara suna kanana na tasiri wajen rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.