Isa ga babban shafi
Jamus

An gano akwai naman Doki cikin wasu nau'in abincin da ake sayarwa a Jamus

Hukumomin kasar Jamus sun ce sun gano naman dawaki a abincin da ake sayar wa ga al’ummar kasar, a Yayin da badakalar sayar wa jama’a naman Dawaki, a maimakon na shanu ke ci gaba da yaduwa a Nahiyar Turai,

Wata Kasuwar Nama a California kasar Amurka
Wata Kasuwar Nama a California kasar Amurka REUTERS/Alex Gallardo
Talla

Wani jami’in gwamnti mai suna Holger Eichele ya ce, binciken da suka gudanar a jahohin kasar, ya gano, 24 cikin abinci 360 da aka gwada, suna dauke da naman na Dawaki.

Ya ce yanzu ba lokaci ne da za a dora laifi kan wani ba, amma hukumomi na kokarin gano wadanda ke da laifi, da ma wadanda ke da hannu a kan batun.

Eichele ya ce har yanzu akwai wasu gwaje gwaje fiye da 1000, da za a gudanar a kayayyaki daban daban ba kawai ga abincin da aka dafa ba, har ma da wuraren dafa abincin da mayankar dabbobin.

Abubuwan da aka gano a binciken sun nuna yadda wasu kamfanonin kasar ta Jamus ke da hannu, a badakalar sayar wa jama’a naman na Dawaki a madadin na shanu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.