Isa ga babban shafi
Italiya-Spain

Kamfanin Nestle ya janye abincinsa saboda Naman doki a wasu kasashen Turai

Katafaren Kamfanin Nestle da ke sarrafa kayan abinci da suka kunshi Nescafe da Madara da kayan abincin yara, ya janye abincinsa daga kasuwannin kasashen Italiya da Spain, bayan wani gwaji da aka yi wanda ya tabbatar da samun naman doki a ciki.

Tambarin kamfanin Nestle da ke samar da kayan Abincin Gwangwani
Tambarin kamfanin Nestle da ke samar da kayan Abincin Gwangwani Reuters
Talla

Mai magana da yawun kamfanin yace yawan naman dokin da aka samu bai zarce kashi guda ba, amma ya zargi wani kamfanin Jamus da ke samar masa da naman a matsayin wanda ya yaudare shi.

Gwamnatocin kasashen Turai sun ce naman Doki baya da illa ga lafiyar Al’umma, amma wannan ya gurgunta lamurra tsakanin masu hidimar Nama da masu saya a kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.