Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Za a binciki naman da ake ci a Turai

KUNGIYAR Kasashen Turai ta bukaci wakilan ta, su gudanar da bincike sosai, a kan dukkan naman da ake sayarwa a kasuwanni. Kungiyar ta dauki wannan matakin ne, don magance matsalar sayarwa da jama’a naman doki da yanzu haka ya jefa yankin cikin rudani.Kwamishinan lafiya na kungiyar, Tonio Borg yace suna bakin kokarin su wajen magance matsalar.Borg yace, yana fatan kwantar da hankalin Yan kasashen Turai, wajen sa ido kan matsalar da ta bullo a cikin ‘yan kwanakin nan, inda aka yi ta baiwa jama’a naman doki ta hanyar da bata dace ba, wanda hakan laifi ne, kuma za a dauki matakan da suka dace don shawo kan matsalar. 

Wani naman da ake bincike a kasar Jamus
Wani naman da ake bincike a kasar Jamus REUTERS/Ina Fassbender
Talla

A kasar Jamus ma, wasu jami’an gwamnati, sun bayyana zargin shiga da kayan Abinci da ba’a fayyace abinda ke kunshe a cikinsu ba.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da ake fargabar yaduwar Naman Doki a nahiyar Turai.

Ma’aikatar kula da harkar Gona da kare hakkin masu cin abinci ta bayyana cewar a ranar Talata ne hukumomi a kasar Jamus suka samu kashedin cewar ana nan ana kokarin shiga da kayan.

Ma’aikatar ta bayyana cewar daga cikin ababen da ake zargin shiga dasu a kasar ta Jamus sun hada da wani babban Sunduki makare da Naman Doki da aka kai cibiyar sarrafa kayan abinci dake a yammacin jihra Rhine-Westphalia ta Arewa, kuma maiyuwa ne sauran kayan abincin su kasance kunshe da naman na Dokin.

Yanzu haka dai hukumomi a jihar na kokarin tantance ko an kammala janye sauran kayan abincin dake kunshe da naman nokin a nasuwanni, da kuma tabbatar da ganin ko akwai naman na doki a cikin kayan da ake zargi.

Wata mai magana da yawun ma’aikatar ta bayyana cewar yanzu haka an cigaba da gwaji, amma ya zuwa yanzu ba’a samu wanda yake kumshe da naman dokin ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.