Isa ga babban shafi
China-Amurka

China ta soki Trump saboda Hong Kong

Kasar China ta yi mummunar suka kan abinda ta kira katsalandan da shugaba Donald Trump na Amurka ke yi mata kan harkokinta na cikin gida dangane da zanga- zangar da ke gudana a Hong Kong bayan da masu zanga-zanga suka yi ta'adi a Majalisar Dokokin yankin na Hong Kong.

Jami'an tsaron Hong Kong na tarwatsa masu zanga-zanga a Majalisar Dokokin yankin
Jami'an tsaron Hong Kong na tarwatsa masu zanga-zanga a Majalisar Dokokin yankin REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Geng Shuang ya bayyana matakin na Trump a matsayin abin takaici.

Shi dai Trump ya bayyana cewar masu neman dimokiradiya ne ke zanga-zangar, amma wasu gwamnatoci basa bukatar dimokiradiyar.

A yayin wani jawabi da ta gabatar, jagorar gwamnatin Hong Kong Carrie Lam ta yi bayyana cewa, "Amfani da karfi wajen tashin hankali da kuma lalata kayan gwamnati da masu zanga-zanga suka yi, bayan sun kutsa kai cikin ginin majalisar, wani abu ne da ya dace mu yi tir da shi saboda babu abinda ke da muhimmanci da ya wuce mutunta doka da oda a Hong Kong. Saboda haka ina fatar cewar al’ummomi da dama za su amince da mu cewar, wannan tashin hankalin da muka gani, ya zama wajibi mu yi tir da shi."

Zanga-zangar Hong Kong ta samo asali ne bayan gwamnatin yankin ta bayyana shirinta na tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci a can, lamarin da al'ummar yankin suka ki amincewa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.