Isa ga babban shafi
Hong Kong

An bukaci jagorar Hong Kong da ta yi murabus

Fitaccen dalibin Hong Kong da ke fafutukar kare hakkin bil’adama, Joshua Wong ya bukaci shugabar gwamnatin yankin, Carrie Lam da ta yi murabus daga mukaminta.

Joshua Wong da aka sallama daga gidan yarin Hong Kong
Joshua Wong da aka sallama daga gidan yarin Hong Kong REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Wong mai shekaru 22 da aka sallama daga gidan yari a ranar Litinin, na cikin wadanda suka jagoranci wata gagarumar zanga-zangar tabbatar da tsarin dimokradiya a shekarar 2014 a Hong Kong.

A yayin zantawa da manema labarai jim kadan da sakin sa daga gidan kaso, Wong ya ce, yana bukatar gajeren lokaci domin gudanar da wani nazari, amma a cewarsa, tabbas zai shiga a dama da shi a sabuwar zanga-zangar adawa da kudirin dokar tasa keyar masu laifi zuwa China domin fuskantar hukunci.

An garkame matashin dalibin ne a gidan yari bayan an same shi da laifin yi wa doka karan tsaye a lokacin  zanga-zangar 2014 wadda ta bukaci gudanar da zabuka cikin tsarin dimokradiya.

A ranar Lahadin da ta gabata, kimanin al’ummar Hong Kong miliyan 2 ne suka fantsama kan tituna domin ci gaba da zanga-zangar adawa da kudirin dokar tasa keyar masu laifin, kodayake jami’an ‘yan sanda sun ce, adadin masu boren bai wuce dubu 338 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.