Isa ga babban shafi
Syria

Mayakan kungiyar IS sun mika wuya

Kimanin mutane dubu biyu, yawancinsu mayakan kungiyar IS ne suka mika wuya ga sojojin da ke samun goyon bayan Amurka a tungarsu ta karshe a gabashin Syria.Mai Magana da yawun dakarun sa kai na Kurdawa a Syria, Adnan Afrin ya ce an mika mutanen da suka baro tungar mayakan IS da ke dada rage karsashi a baya bayan nan ga dakarun sa kan don a bincikesu.

Mayakan Jihadi a kasar Syria
Mayakan Jihadi a kasar Syria REUTERS/Rodi Said
Talla

Dakarun da ke samun goyon bayan Amurka sun shafe lokaci suna kokarin murkushe mayakan jihadi na IS amma dimbin fararen hula, maza da mata da yara dake kwararowa daga kauyukan da ke gabar kogi ya sa suka rage mata kaimi.

Bayan sun gargadi mayakan na IS da cewa lokaci ya kure, suka yi musu diran mikiya a Lahadin da ta gabata, inda suka yi ta luguden wuta ta sama da kasa a yankin Baghouz, dare uku a jere, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mayakan IS da dama.

Dubban mayakan na IS sun mika wuya a talatan nan, biyo bayan ruwan wuta da suka sha daga dakarun sa kai

Yanzu abin da ya rage daga daular da IS ta ayyana a matsayin nata a shekarar 2014, a Baghouz, dake gabashin Syria shine tsumokarar tentuna dake sansanin nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.