Isa ga babban shafi
AMurka-Syria

Kasashen Turai sun mayar wa Trump martani kan Syria

Kasashen Birtaniya da Jamus da Faransa sun mayar da martani kan aniyar shugaban Amurka, Donald Trump ya ta janye dakarun kasar daga Syria.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Mark Wilson/Getty Images/AFP
Talla

Faransa da Birtaniya da suka lashi takobin ci gaba da wanzar da dakarunsu a Syria, sun ce, har yanzu akwai-sauran -rina-a-kaba a yaki da Kungiyar ISIS, sabanin ikirarin Trump da ke cewa, an ci karfin ta.

Kimanin dakarun Amurka dubu 2 ke jibge a Syria, in da akasarinsu ke aikin bada horo da shawarwarin da ke taimaka wa dakarun kasar wajen yaki da Kungiyar ISIS, yayin da Birtaniya da Faransa ba su bayar da alkaluman nasu dakarun da ke cikin kasar ba.

Mai magana da yawun Firaministar Birtaniya ya ce, za su ci gaba da nuna goyon baya ga rundunar hadaka ta kasashen duniya da zummar murkushe yunkurin ISIS na kafa daula, in da ya ce, irin wannan hadaka ta haifar da da-mai-ido, amma har yanzu akwai-sauran-rina-a-kaba.

A bangaren Jamus kuwa, Ministan Harkokin Wajenta, Heiko Maas cewa ya yi, matakin janye dakarun na Amurka zai yi illa ga nasarar da aka samu akan ‘yan ta’addan da har yanzu ke ci gaba da rike da wasu yankuna a gabashin Syria.

Wasu daga cikin mambobin Majalisar Dokokin Amurka sun gargadi cewa, matakin na Trump ka iya bai wa Turkiya kwarin gwiwar kaddamar da hari kan dakarun Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka a yaki da ISIS.

A ranar Laraba ne shugaba Trump ya ce, sun samu nasarar murkushe ISIS, don haka lokaci ya yi da dakarunsu za su koma gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.