Isa ga babban shafi
Amurka- syria

Amurka ba za ta taimaka wa Syria ba- Pompeo

Amurka ta ce, ba za ta bada kudaden taimakon sake gina Syria mai fama da yake-yake ba muddin Iran ta ci gaba da zamanta a kasar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo a fadar White House
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo a fadar White House REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

A yayin zantawa da Kungiyar da ke Goyon Bayan Yahudawan Isra’ila a birnin Washington, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya lashi takobin daukan matakan karfi da yaji na tunkarar manufofin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya, in da ya ce, ta mayar da Syria fagen daga.

A cewar Pompeo, gwamnatin Syria ce ke da alhakin koran Iran daga kasarta domin kuwa ita ce ta ba ta wurin zama.

Sakataren Harkokin Wajen na Amurka ya ce, matukar Syria ba ta tabbatar da ficewar dakarun da ke samun goyon bayan Iran ba a kasar, to babu shakka, Amurka ba za ta ba ta ko sisi ba na sake gina kasarta.

Ana kallon kalaman Pompeo a matsayin fashin baki kan dalilin tsoma bakin Amurka a yakin basasar Syria da alkaluma ke cewa, ya salwantar da rayukan mutane kusan dubu 360 tun shekarar 2011.

A cewar Pompeo, shugaba Bashar Al-Assad ya kara samun karfi ne sakamakon taimakon da Iran da Rasha ke ba shi.

Tun zamanin mulkin Barack Obama ne, Amurka ta bada umarnin daukan matakan soji da zummar kakkabe mayakan Kungiyar ISIS da ke kaddamar da hare-hare a Syria da wasu kasashen yammaci, yayin da Pompeo ke cewa, murkushe wann an kungiya shi ne babban abin da ke gabansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.