Isa ga babban shafi
G20-Argentina

Taron G20 zai tabo batun rikice-rikicen da duniya ke fuskanta

Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Argentina don halartar taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na duniya da za a fara gudanarwa cikin karshen makon nan.Ana sa ran batutuwa masu alaka da rikicin kasuwancin manyan kasashen da matsalar dumamar yanayi su mamaye taron.

shugabannin kasashen duniya fiye da 20 ne za su hallara a taron ciki har da kasashen da basa cikin kungiyar amma kuma aka gayyacesu don bada tasu gudunmawa a taron.
shugabannin kasashen duniya fiye da 20 ne za su hallara a taron ciki har da kasashen da basa cikin kungiyar amma kuma aka gayyacesu don bada tasu gudunmawa a taron. France24
Talla

Ana saran dai batun kwace jiragen ruwan Ukraine da Rasha ta yi na baya-bayan nan ya shiga cikin jadawalin batutuwan da za a tafka muhawara kansu yayin taron, haka zalika batun kasuwancin China da Amurka dama matakan yakar dumamar yanayi.

Tuni dai sanarwa ta fita da ke nuna cewa Donald Trump na Amurka da Xi Jinping na China za su gana kan kasuwanci, haka zalika fadar Kremlin ta tabbatar da cewa Vladimir Putin zai gana da Trump.

A bangare guda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi gargadin karkatar da abin da ya dace a tattauna a taron zuwa wani batu daban, wanda ya ce matukar ba a tattauna abubuwan da suka dace ba, taron na G20 zai tashi a banza.

A cewar Macron wanda ya isa Argentina gabanin fara taron a jibi Asabar, kamata ya yi a samar da mafita kan rikice-rikicen da suka dabaibaye kasashen musamman kan batun kasuwanci da sauyin yanayi, maimakon mayar da taron damar zafafa rikici tsakanin kasashen.

A bangare guda Vladimir Putin ya sha alwashin ganawa da Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman kan batun kisan Jamal Khashoggi yayinda wannan taron zai zamo ganawar Yariman da Erdogan na farko tun bayan kisan dan jaridar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.