Isa ga babban shafi
Rasha-Afghanistan

Rasha zata jagoranci sulhu tsakanin Afghanistan da Taliban

Jami’an Rasha sun ce wata tawaga daga gwamnatin Afghanistan za ta halarci tattaunawar sulhu da Taliban, a ranar 9 ga wannan wata a birnin Moscow. To sai dai wannan sanarwa ta Rasha ta zo ne a yayinda rahotanni ke cewa, har yanzu kungiyar Taliban bata tsaida shawara kan tura wakilanta zuwa taron ba.

TALIBAN
TALIBAN DR
Talla

A ranar Asabar da ta gabata Rasha ta ce shugaban Afganistan Ashraf Ghani, ya amince zai aika tawagar da zata wakilci gwamnatin kasar a tattaunawar sulhu da kungiyar Taliban a karkashin jagorancin kasar ta Rasha a birnin Moscow.

Sai dai kawo yanzu ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Afghanistan bata ce za ta aika da tawagarta zuwa taron ba, illa hukuma ta musamman kan tabbatar da zaman lafiya da gwamnatin da kasar ta Afghanistan ta kafa, wadda ta ce za ta aike da jami’an 4 don halartar tattaunawar, kamar yadda kakakinta Sayed Ihsan Taheri ya tabbatar.

A bangaren kungiyar Taliban kuwa, kakakinta Sebagtullah Ahmadi ya ce har yanzu suna tataunawa kan matakin tura tasu tawagar ko akasin haka.

Tun a watan Agustan da ya wuce, Rasha ta yi yunkurin ganin tattaunawar ta gudana, inda ta gayyaci kasashe 12 da kungiyar ta Taliban, amma shugaba Ashraf Ghani yayi watsi da tayin, inda ya ce tilas sai dai tattaunawar ta gudana a karkashin jagorancin Afghanistan.

Wasu daga cikin kasashen da Rasha ta gayyata zuwa tattaunawar sulhun sun hada da India, Iran Pakistan, China da kuma Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.