Rasha za ta shiga tsakani a rikicin Taliban da Afghanistan
Rasha za ta zamo mai shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya game da rikicin Afghanistan inda za ta karbi wakilcin bangarorin biyu a ranar 9 ga watan nan na Nuwamba wanda ake fatan ya kawo karshen rikicin kasar da aka shafe shekaru ana tafkawa.
Wallafawa ranar:
A cewar Rasha ilahirin bangarorin kungiyar ta Taliban da bangaren gwamnati karkashin shugaba Ashraf Ghani sun amince da tura wakilai don tattaunawar wadda ita ce irinta ta farko da Taliban da amince da gudanarwa.
Sai dai ministan harkokin wajen Afghanistan Sebhgatullah Ahmadi ya ce kawo yanzu bazu kammala cimma yarjejeniya game da tattaunawar ba.
A bangare guda wannan ne karon farko da Taliban ta amince da tattaunawar kawo karshen rikicin na su da aka shafe shekaru ana fafatawa ko da dai ilahirin bangarorin biyu sun aminta da tsagaita wutar da suka yi watannin baya wanda a lokacin gwamnati ta bukaci dorewarta amma Taliban ta Bijire.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu