Isa ga babban shafi
Amurka-China

China na bukatar Amurka ta rika sassauci a harkar ciniki

Gwamnatin China ta bukaci Amurka da ta daina daukan matakan fin-karfi wajen harkokin da suka shafi cinikayya da kasashen duniya.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo da Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo da Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi Andy Wong/Pool via Reuters
Talla

Ministan Harkokin Waje na China, Wang Yi ya shaida wa takwaransa na Amurka Mike Pompeo a lokacin da ya yada zango a Beijing a sawu na karshe a rangadin kasashen Asiya da yake yi .

Wang Yi ya shaida Pompeo cewa Amurka ta daina daukan matakan kawo rudani game da karin haraji kan kayayyakin da China ke kai mata.

Ya kuma zargi Amurka da katsalandan cikin harkokin yankin Taiwan da ke cin gashin kansa, wanda kasar China ke kallo a matsayin yankin ‘yan tawaye da daukan wasu matakai da ke yi wa China zafi.

Ministan waje na Chinan ya ce, matakan da Amurka ke dauka shakka babu na iya kai ga sukurkucewar zumunci tsakanin China da Amurka.

Yana mai cewa ya dace kasashen biyu su nemi kara dankon zumunci ne tsakanin su maimakon yi wa juna makarkashiya.

Mike Pompeo ya fadi cewa yana Beijing ne don tattaunawar fahimtar juna tsakanin kasashen biyu.

A cewar Pompeo, babban burin Amurka shi ne tsarkake yankin Korea daga makaman Nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.