Isa ga babban shafi
MDD

Shugabannin kasashen duniya na taro a birnin New York

Shugabannin kasashen duniya na halartar babban taro a zauren Majalisar Dinkin Duniya kashi na 73 a birnin New York na Amurka, in da suke gabatar da  jawabi kan halin da duniyar ke ciki.

Shugabannin Kasashen Duniya a Zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York
Shugabannin Kasashen Duniya a Zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Cikin batutuwan da za su mamaye taron na bana sun hada da kwance damarar nukiliyar Koriya ta Arewa da yarjejeniyar Iran da rikicin Israila da Falasdinu da yakin Syria da Yemen da Libya da safarar baki da kuma rikicin kasuwanci.

Cikin shugabannin da za su fara jawabi a ranar Talata har da shugaba Donald Trump na Amurka da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

A bangare guda, shugabannin  sun kaddamar da taro kan yadda za a shawo kan matsalar sauyin yanayi,  in da suka bukaci gaggauta daukar matakan da zasu rage matsalar.

Yayin da kasar Poland ke shirin daukar nauyin taron kasashe da kungiyoyin da ke yaki da dumamar yanayi a watan Disamba mai zuwa, shugabar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da dumamar yanayi, Patricia Espinosa ta bukaci kasashen duniya da su hada kansu wajen tabbatar da rage ayyukan da suke haifar da sauyin yanayi akalla da maki 2 na ma’aunin celcius kamar yadda aka amince a taron Paris na shekarar 2015.

Jami’ar ta ce, kasashen duniya basa mutunta yarjejeniyar, ganin alkawarin da suka dauka a taron na ganin an rage dumamar yanayin da kashi 3 nan da shekarar 2100.

Espinosa ta ce,  taron da aka gudanar a Bangkok wannan watan bai cimma wata yarjejeniya ba saboda haka mahalarta taron na da babban aiki a gabansu wajen samun mafita.

Shi ma gwamnan California, Jerry Brown yace magance matsalar dumamar yanayi na da matukar tasiri wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.