Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Manyan kasashe na barazana ga yarjejeniyar Paris

Kananan Kasashen Duniya sun zargi Amurka da kawayenta da haifar da tarnaki wajen aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a birnin Paris da zummar magance matsalar dumamar yanayi. Kasashen sun yi zargin ne a yayin kammala taron gaggawa da ya gudana a birnin Bankok a karshen mako.

Manyan kasashen duniya na kan gaba wajen fitar da hayaki mai gurbata muhalli
Manyan kasashen duniya na kan gaba wajen fitar da hayaki mai gurbata muhalli Reuters/Stringer
Talla

Kwararru daga sassan duniya sun kammala tattaunawa a taron na birnin Bankok, in da suka mayar da hankali kan samar da dokokin da za su tilasta wa kasashe aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayin da aka cimma a birnin Paris.

Sai dai tattaunawar ta gamu da tangarda ta fannin kokarin ganin kasashen duniya sun bada hadin-kai wajen bada gudun mawar kudaden magance matsalar.

Wakilan kasashen duniya matalauta a taron, sun ce, Amurka da kasashen yammaci masu karfin tattalin arziki sun gaza matuka wajen bada gudun mawar kudaden tunkarar matsalar.

A cewar shugaban wakilan kananan kasashen, Amjad Abdulla, manyan kasashen ne ke da alhakin fitar da hayaki mai gurbata muhalli, in da akasarinsu suka samu arziki ta hanyar gurbata muhallin.

Abdulla ya kara da cewa, suna fuskantar bala’in sauyin yanayin, lamarin da ka iya haddasa bacewar wasu kasashen a dadalilin tunbatsar teku muddin aka gaza daukan matakin kawo ci gaba a yarjejeniyar ta birnin Paris nan da karshen shekarar da muke ciki.

Yarjejeniyar wadda aka cimma a shekarar 2015, na da nufin rage gurbata muhalli a duniya baki daya da akalla digiri biyu a ma’aunin Celcius.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.