Isa ga babban shafi
Duniya

Yaki da labaran karya da ake yadawa ta kafofin sada zumunta a Duniya

Manyan Kamfanonin yada labarai 24 na Duniya suka kulla wani kawance a taron da suka gudanar a Brazil domin yaki da labaran karya da ake yadawa ta kafofin sada zumunta.Kamfanonin sun hada da na dillancin labaran Faransa AFP da Metro Brasil.

Shafin sada zumunta na Facebook
Shafin sada zumunta na Facebook 路透社
Talla

Taron da ya gudanar a Brazil ya sanya sunan kawancen kamfanonin yada labaran ‘Comprova’ wanda zai bada damar gudanar da bincike domin gano labaran karya a karkashin wani hadin kan da ya kunshi Kungiyar Binciken yan Jaridar Brazil da kuma tallafin kudade daga kamfanonin google da facebook.

Taron yace an horar da Yan Jaridu da kuma Editocin su wajen tantance labaran karya da ake yadawa a yanar gizo da zummar karkatar da ra’ayoyin jama’a.

Kungiyar ta Comprova zata mayar da hankali kan labaran da aka riga aka yada su ko kuma suka yi fice a kafofin sada zumunta, yayin da Editoci za su mayar da hankali wajen dakushe kaifin irin wadanan labaran.

Claire Waddle, Shugabar kungiyar tace za suyi amfani da kafar Whatsapp musamman ganin yadda mutane sama da miliyan 120 ke amfani da shi a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.