Isa ga babban shafi
facebook

EU ta gayyaci shugaban Facebook kan Trump

Majalisar Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci shugaban kamfanin dandalin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg da ya je ya yi ma ta bayani kan bayanan cewar wani kamfani da ke yi wa shugaban Amurka Donald Trump aiki ya tatsi bayanan mutane miliyan 50 da ke amfani da shi.

Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg
Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg REUTERS/Mariana Bazo
Talla

Ana zargin kamfanin mai suna Analytica da ke Birtaniya da tatsar bayanan ne a lokacin yakin neman zaben shugaba Trump a shekarar 2016.

Tuni Majalisar ta bukaci gudanar da binciken gaggawa kan lamarin.

Shugaban Majalisar Dokokin Antonio Tajani, ya ce ya zama wajibi kamfanin Facebook ya yi wa wakilan mutane miliyan 500 da ke Turai bayani kan yadda aka tatsi bayanansu.

Ita ma Majalisar Birtaniya ta bukaci shugaban Facebook Mark Zukerberg ya je ya yi ma ta bayani akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.