Isa ga babban shafi
Afrika

Gutteres na ziyarar goyon baya ga jami'an wanzar da zaman lafiya a Mali

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya isa kasar Mali domin goyawa dakarun da ke aikin samar da zaman lafiya baya, bayan yan ta’adda sun kashe da dama daga cikinsu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress. REUTERS/Mike Segar
Talla

Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya tarbi Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a filin jirgin saman Bamako, inda suka ziyarci cibiyar dakarun samar da zaman lafiya ta MINUSMA wurin da akayi bikin ranar aikin samar da zaman lafiya ta duniya.

Guterres yayi amfani da damar wajen yabawa sojoji maza da mata da suka bada gudumawa wajen sadaukar da rayukan su a kasar.

Akalla Sojoji da yan sanda da kuam fararen hular dake aiki a karkashin dakarun Majalisar domin tabbatar da zaman lafiya 160 aka kashe tun bayan girke su a shekarar 2013, kuma shine adadi mafi girma a aikin da Majalisar take gudanarwa a duniya.

Sanarwar Majalisar tace ziyarar ta kwanaki biyu zata bashi damar yin azumin watan Ramadana a Malin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.