Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya za ta karfafa rundunarta a Mali

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai bukatar daukar sabbin matakai domin karfafa rundunar wanzar da zaman lafiya ta Minusma da ke aiki a Mali sakamakon yawaitar hare-hare akan dakarun rundunar.

Matakin Majalisar na zuwa ne bayan jerin hare-haren da ke ci gaba da lakume rayukan sojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Malin.
Matakin Majalisar na zuwa ne bayan jerin hare-haren da ke ci gaba da lakume rayukan sojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Malin. Kacper Pempel / Reuters
Talla

A wani zama na musamman da ya gudanar a jiya, Kwamaitin Tsaron ya bukaci Canada da ta gaggauta cika alkawarin da ta dauka na aikewa da dakaru da kuma jiragen yaki zuwa kasar ta Mali.

A karshen makon jiya, ‘yan bindiga sun kai hari kan dakarun na MDD a garin Tumbuktu da ke arewacin kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.