Isa ga babban shafi
Mali

Fararen hula 12 sun mutu a harin ta'addanci a Mali

Akalla fararen hula 12 sun rasa rayukansu a arewacin kasar Mali, a harin da wasu mayaka suka kai kan wata kasuwa da ke garin Boulekessi a gaf da iyakar kasar ta Mali da Burkina Faso.

Wasu train jami'an tsaron Mali kenan da ke aikin Sintiri a yankin da ke fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi.
Wasu train jami'an tsaron Mali kenan da ke aikin Sintiri a yankin da ke fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi. Philippe Desmazes/AFP
Talla

Wata majiyar rundunar sojin ta Mali ta ce ana fuskantar wahalar sha'anin sadarwa da garin na Boulekessi, abinda yasa har yanzu ba’a kai ga tantance ko an samu karuwar wadanda suka hallaka ba, da kuma wadanda suka jikkata.

Mali dai na fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi masu da'awar jihadi, wanda a lokuta da dama kan haddasa asarar dubban rayuka.

Haka zalika kasar na cikin kasashen Sahel da aka kafa runduna ta musamman don yakar ayyukan ta'addancin da suka yi kamari a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.