Isa ga babban shafi
Rasha

Kasashen Yamma sun kori jakadun Rasha 114

Amurka da Kungiyar Kasashen Turai da kawayensu a duniya, sun kori jakadun Rasha 114 a matsayin mayar da martani kan zargin da ake yi wa kasar na kai hari da makami mai guba kan wani jami’in leken asiri a Birtaniya.

Gwamnatin Shugaban Rasha Vladimir Putin ta sha alwashin daukan ramako kan matakin koran jadakunsa a kasashen duniya
Gwamnatin Shugaban Rasha Vladimir Putin ta sha alwashin daukan ramako kan matakin koran jadakunsa a kasashen duniya Anatoly Maltsev/Pool via REUTERS
Talla

Alkaluma sun nuna cewar, Amurka ta kori jakadu 60, kungiyar kasashen Turai 30, yayin da kuma kawayensu da suka hada da Canada da Ukraine da Albania da Australia suka bi sahu wajen korar jakadun Rasha da ke kasashensu.

Gwamnatin Rasha ta ci gaba da musanta zargin amfani da makamin mai guba kan Sergei Skripal da ‘yarsa, wadanda a yanzu haka suke fama da matsanancin rashin lafiya.

A karon farko kenan da ake ganin an yi amfani da wannan guba ta Novichok a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

Rasha dai ta ce, za ta dauki matakin ramako kan kasashen da suka kori jakadunta bayan sun biye wa Birtaniya da ta hakikance kan kaddamar da harin na guba a lardinta na Salisbury.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.