Isa ga babban shafi
Birtaniya

EU ta mara baya a zargin Rasha da harin guba a Birtaniya

Kungiyar tarayyar Turai ta kara jaddada goyon bayanta ga Birtaniya dangane da batun zargin da ta ke kan Rasha na amfani da guba kan tsohon dan leken asirinta da ke aiki da Birtaniyar.Matakin na EU na zuwa a dai dai lokacin da wasu tarin kwararru kan makamai suka isa kasar ta Birtaniya don daukar samfurin gubar da aka yi amfani da ita kan Sergei Skripal don yin gwaji.

Wani zaman tattaunawar gaggawa kenan a zauren Majalisar Dinkin Duniya da Birtaniya ta kira don tattaunawa game da batun yunkurin kisan jami’in na ta kuma tsohon dan leken asirin Rasha Sergei Skripal.
Wani zaman tattaunawar gaggawa kenan a zauren Majalisar Dinkin Duniya da Birtaniya ta kira don tattaunawa game da batun yunkurin kisan jami’in na ta kuma tsohon dan leken asirin Rasha Sergei Skripal. REUTERS/Shannon Stapleton
Talla

Wata sanarwar hadaka da ministocin harkokin wajen kasashen na EU suka fitar, ta ce suna da yakinin cewa tabbas Rashan ta aikata abin da Birtaniyar ke zarginta kan Sergei Skripal da ‘yarsa Yulia a garin Salisbury ranar 4 ga watan Maris.

EU ta kuma tabbatar da cewa za ta mara baya har sai ta tabbatar da an aiwatar da hukunci kan masu amfani makamai masu guba ciki kuwa har da na batun Birtaniyar.

Tuni dai batun yunkurin kisan na Sergei Skripal ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin kasashen Rasha da Birtaniyar bayan da kowannesu ya sallami wani kaso mai yawa na jakadun diflomasiyyar kowanne.

Ko da ya ke dai kai tsaye shugaban Rasha Vladimir Putin ya musanta zargin na Birtaniya inda ya ce baya da masaniya kan gubar hasalima kasarsa ba ta da sinadaran hada nau'in gubar ta Novichok.

Haka zalika ko a yau Litinin Dmitry Peskov ya yi gargadin cewa Birtaniyar ba ta wata hujja da ke nuna cewa Rashan na da hannu a amfani da gubar kan tsohon dan leken asirin na ta, yana mai cewa idan har da gaske ne to ta nuna hujja ko kuma ta nemi yafiya ga Rashan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.