Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta yi barazanar kai hare-hare a Syria

Amurka ta yi barazanar kai hare-hare kan kasar Syria, matukar dai Majalisar Dinkin Duniya ta gaza samar da tsagaita wuta a yankin Ghouta da ke kasar Syria.

Amurka ta ce, matukar yarjejeniyar tsagaita wuta ta gaza a Syria, to lallai za ta kaddamar da farmaki kan dakarun kasar
Amurka ta ce, matukar yarjejeniyar tsagaita wuta ta gaza a Syria, to lallai za ta kaddamar da farmaki kan dakarun kasar Vadim Grishankin / RUSSIAN DEFENCE MINISTRY / AFP
Talla

A marecen jiya litinin ne Amurka ta gabatar wa Kwamitin Tsaro na Majalisar da wani sabon daftari, da ke neman a gaggauta tsagaita wuta domin isar da kayayyakin jinkai ga jama’a, kuma matukar kwamitin tsaron ya gaza to lalle kuwa Amurka za ta yi gaban kanta.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikky Haley ta ce, tsagaita wutar da Kwamitin Sulhu na ya bukata a baya ya gaza yin aiki don samun damar shigar da kayakin agaji ga dubban fararen hular da ke bukatar agajin abinci da magunguna, sakamakon yadda Syria bisa goyon bayan Rasha ta ki mutunta yarjejeniyar tare da ci gaba da luguden wuta a yankin na gabashin Ghouta.

Haley ta ce, yanzu za su gabatar da wata sabuwar bukatar tsagaita wutar ta yadda babu yadda za a yi ma ta hawan kawara, in da ta zargi Rasha da rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar duk da cewa ta kada kuri’ar amincewa da hakan a gaban Majalisar Dinkin Duniyar.

Jakadiyar Amurkan ta ce, ko bayan da Rashan ta amince da tsagaita wutar, sai da ta kai wasu farmaki na bama-bamai har sau 20 a biranen Damascus da Ghouta.

Haley ta kuma bukaci Majalisar ta gaggauta daukar mataki kan duk wata kasa da ta yi yunkurin wargaza tsagaita wutar da ma duk wata kasa da ta kai hare-hare da makamai masu guba kan al’umma a Syrian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.