Sarkin Jordan zai gana da Abbas kan rikicin Falasdinu
A ranar Litinin mai zuwa ne Sarkin Jordan Abdullah na biyu zai kai ziayarsa ta farko cikin shekaru biyar a birnin Ramallah da ke gabar Yamma da Kogin Jordan, in da zai gana da shugaban Falasdinu Mahmud Abbas.
Wallafawa ranar:
Wani babban Jami’i a kungiyar Fatah ta Abbas, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, shugabannin biyu za su zanta kan yadda za a farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
Tun a shekarar 2014 ne, tattaunawa tsakanin bangariorin biyu ta tsaya cak.
Kasar Jordan ta soma baki a cikin watan jiya don samar da masalaha kan rikicin da ya barke tsakanin jami’an tsaron Isra’ila da Falasdinawa a harabar Masallacin Haram al-Sharif da ke tsohon birnin Kudus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu