Jamus ta zargi Trump da kitsa rikicin Larabawa
Kasar Jamus ta zargi shugaban Amurka Donald Trump da kitsa rikici tsakanin kasashen Larabawa domin ganin an samu cinikin makamai.
Wallafawa ranar:
Ministan Harkokin Wajen Jamus Sigmar Gabriel ya ce, kwangilar makaman da Saudiya ta bai wa Amurka na daga cikin dalilan da suka haifar da rikicin da aka samu tsakanin Saudiyar da kawayenta musamman kasar Qatar
Gabriel ya ce, ya na fargabar abin da zai biyo baya sakamakon wannan matsalar da aka samu a fadin yankin kasashen Larabawa baki daya.
A farkon makon ne kasashen Saudiya da Masar da Yemen da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrai suka katse hulda da Qatar tare da rufe kan iyakokinsu na sama da na ruwa da na kasa da Qatar.
Daukan wannan mataki na zuwa bayan sun zargi Qatar da tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'adda, zargin da ta musanta.
Shugaba Donald Trump ya ce, ziyarar da ya kai Saudiya ce ta haifar da matakin da aka dauka kan kasar Qatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu