Kuwaiti zata warware rikicin Qatar da sauran kasashen Larabawa
Sarkin kasar Kuweiti Sheikh Sabah al-Ahmad Al-Sabah ya isa birnin Riyad na Saudiyya, domin shiga tsakani da nufin shawo kan rikicin diflomasiyyar da ya barke tsakanin wasu kasashen Larabawa da kuma Qatar.
Wallafawa ranar:
Rikicin da ya sanya kasashen da suka hada da Hadaddiyar daular Larabawa, Masar, Baharain, Libya, Yemen, Maldives a karkashin jagorancin Saudiyya suka yanke alaka tsakaninsu da kasar ta Qatar.
Daga cikin matakan da suka dauka dai akwai dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakaninsu da ita, sai kuma rufe iyakar da ke tsakanin Qatar din da Saudiyya.
Tuni dai ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohamed Bin Abdul Rahman, ya ce kasar a shirye take, ta shiga tattaunawar sulhu da sauran kasashen domin warware sabanin da ke tsakaninsu, inda y ce Qatar ba ta da niyyar daukar wani mataki na ramuwar gayya akansu domin zai shafi rayuwar al’ummomin kasashen da ke cikin kungiyar hulda da juna a yankin Gulf baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu