Isa ga babban shafi
Amurka

FBI za ta ci gaba da binciken kutsen Rasha a zaben Amurka

Sabon shugaban hukumar bincike ta FBI a Amurka na rikon kwarya, Andrew McCabe ya shaidawa Majalisar kasar cewa, korar James Comey ba zai haifar da cikas ba wajen ci gaba da gudanar da bincike kan kutsen da ake zargin Rasha ta yi a zaben Amurka.

Sabon shugaban FBI na rikon kwarya Andrew McCabe
Sabon shugaban FBI na rikon kwarya Andrew McCabe REUTERS/Eric Thayer
Talla

A wani zaman sauraren bahasi, sabon shugaban hukumar ta FBI ya shaida wa kwamitin tara bayanan sirri na Majalisar Dattawan kasar cewa, kawo yanzu babu wani yunkuri na dakatar da bincikensu kan zargin kutsen Rasha a zaben 2016.

McCabe ya ce, babu mai dakatar da jami’an FBI maza da mata wajen gudanar da ayyukan da suka dace.

Mukaddashin shugaban na FBI ya bayyana irin yadda ya ke mutunta Mista Comey da shugaba Donald Trump ya sallama, in da ya ce, yana girmama shi sosai kamar yadda daukacin ma’aikatan hukumar ke ci gaba da ganin mutuncinsa.

Kalaman McCabe sun jefa shakkun kan ikirarin fadar White House da ta ce, Comey ya rasa tagomashinsa a idon ma’aikatansa.

Korar James Comey a matsayin jagoran FBI ta haddasa cecekucen siyasa a Amurka, in da ‘yan jami’ayar Democrat ke cewa, Donald Trump ya dauki mataki ne don kawo cikas a binciken kutsen Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.