Isa ga babban shafi
Amurka

Trump zai binciki zaben Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, zai bayar da umurnin gudanar da bincike dangane da zargin cewa akwai milyoyin mutane da suka jefa kuri’unsu a zaben da ya gabata duk da cewa ba su cancanci hakan ba.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Duk da cewa ya yi nasara a zaben na watan Nuwamban bara, to amma har yanzu Trump na ci gaba da zargin cewa an yi ma sa magudi sakamakon bai wa milyoyin mutane damar jefa kuri’a ta hanyar da ba ta dace ba.
 

Donald Trump dai na zargin cewa an tafka magudin ne ta hanyoyi da dama, da suka hada da yi wa milyoyin mutane rajista domin ba su damar yin zabe a jihohi biyu mabambanta, yayin da kuma aka yi wa wasu dubban matacci rajista.

Trump ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ‘’bai kamata jama’a su yi mamaki a game da wannan zargi da ya ke yi ba, domin akwai hujjojin da ke tabbatar da haka’’.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Sean Spicer ya ce, zargin da Trump ke yi ya dogara ne akan hujjoji, kuma wannan bincike zai gano gaskiyar abin da ya faru.
 

To sai dai ba shugaban kasar ta Amurka ne kawai ya yi irin wannan zargi ba, domin a can baya jami’ar Old Dominion University da ke kasar ta fitar da wani rahoton bincike da ke cewa kashi 14 na wadanda suka yi zabe ba Amurkawa ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.