Isa ga babban shafi
Amurka

Zamanin gwamnatin Trump a Amurka

A yau juma’a za a rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45, inda zai gaji Barack Obama wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 8. Trump ya yi alkawalin samar da canji tare da hada kan Amurkawa a jawabin da ya gabatar a gidan tarihin Lincoln.

Shugaban Amurka Donald Trump da mai dakinsa Melania a Washington fadar gwamnatin Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump da mai dakinsa Melania a Washington fadar gwamnatin Amurka MANDEL NGAN / AFP
Talla

Amurkawa 800,000 aka kiyasta za su halarci bikin rantsar da Trump wanda ba a taba tunanin zai zama shugaban Amurka ba.

Za a rantsar da Trump ne da littafin bible na Abraham Lincoln.

Trump mai shekaru 70 a duniya, ya fi shugabannin Amurka yawan shekaru da aka rantsar da su. Kuma shugaban Amurka na farko da bai taba rike mukamin siyasa ba.

Donald Trump zai karbi ragamar mulkin ne a cikn wani yanayi na rashin kwarewa a siyasa da diflomasiyya balantana aikin soji a wannan kasa mafi girma a siyasa da kuma tattalin arziki a duniya.

Akwai ‘yan majalisa da kuma manyan shugabannin jam’iyyarsa ta Republican da dama da suka ce za su kaurace wa bikin rantsar da shi, yayin da dubban mutane a sassa daban daban na kasar suka shirya gudanar da zanga-zanga a yau juma’a, domin adawa sabon shugaban na Amurka.

Dubban Amurkawa ne suka shirya gudanar da zanga-zanga a birnin Washington a yau juma’a da ake shirin rantsar da Trump.

Daga cikin masu shirin gangamin a lokacin rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka sun hada da wadanda ke da sabani da shi kan bakin haure da Musulmi, da kuma masu kare shirin inshoran lafiya ta Obama da batun gina katangar da za ta raba Amurka da Mexico.

Magoyan bayan shahararren dan kasuwar, sun yi amannar cewa Trump ne kadai zai iya biya wa Amurkawa muradunsu.

Magoya bayan Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado
Magoya bayan Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado wikimedia.org/Gage Skidmore

Sakataran tsaron Amurka mai barin gado Jeh Johnson ya ce an shirya matakan tsaro, domin kaucewa samun tashin hankali a wajen bikin rantsuwar, inda za a tanadar wa magoya baya da masu adawa da Trump wajen zama na daban.

Akalla jami’an tsaro dubu 28 ne za su bada tsaro, yayin da kungoyoyi kusan 30 ke cewa za su yi duk mai iyawa wajen ragewa bikin armashi.

Ana dai ganin bikin rantsar da Trump ba zai yi armashi ba kamar na Barack Obama a 2009 inda mutane akalla miliyan 2 suka yi cikar kwari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.