Isa ga babban shafi
Venezuela

Mutane 20 sun mutu a zanga-zangar Venezuela

Alkaluman mutanen da suka gamu da ajalinsu a wata zanga-zangar adawa da gwamnatin Venezuela sun kai 20 bayan wata sabuwar arangama ta barke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangara a birnin Caracas.

Masu zanga-zangar na son shugaba Nicolas Maduro ya sauka daga kujerarsa
Masu zanga-zangar na son shugaba Nicolas Maduro ya sauka daga kujerarsa REUTERS/Isaac Urrutia
Talla

Jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta harba hayaki mai sa kwalla, in da kuma wasu zaune gari banza suka yi ta harba bindiga kan gidajen al’umma kamar yadda kamfanin Dillancin Labarana Faransa na AFP ya rawaito.

Sai dai wasu rahotanni na cewa, mutane 8 sun rasu ne sakamakon fadowar wayar wutar lantarki kan masu zanga-zangar ganin shugaba Nicolas Maduro ya sauka daga kujersa.

'Yan adawa na zargin gwamnati da hayo 'yan daba don kai musu farmaki a yayin zanga-zangar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.