Masu zanga-zanga sun gwabza fada da 'yan sanda a kasar Venezuela
A kasar Venezuela masu zanga-zanga sun yi taho mu gama da ‘yan sanda a birnin Caracas, wanda shine karo na hudu a cikin mako daya da jama'a ke nuna kyamar Gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.
Wallafawa ranar:
A wannan karo masu zanga-zangan na kara nuna rashin amincewarsu game da matakin da Gwamnatin ta dauka na haramtawa shugaban ‘yan adawa na kasar Henrique Capriles rike duk wani ofis na tsawon shekaru 15.
Dubban mutane ne dai suka halarci zanga-zangan na yau.
Shi dai jagoran adawan Capriles mai shekaru 44 a zaben shugabancin kasar a shekara ta 2013, da rata kadan aka fi shi da kuri'u.
Ana ganin Gwamnatin kasar ta haramta masa rike Ofis na tsawon shekaru ne don kada ya ke fitowa takaran shugabancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu