Isa ga babban shafi
Venezuela

‘Yan adawa na zanga-zanga a Venezuela

‘Yan Adawa a Venezuela sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga da za ta kifar da gwamnatin Nicolas Maduro duk da hasarar rayuka biyu da aka samu a arangama da suka yi da ‘yan sanda a ranar Laraba.

'Yan adawa na zanga-zangar adawa da Maduro a Caracas
'Yan adawa na zanga-zangar adawa da Maduro a Caracas REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Rahotanni sun ce an kashe wani matashi mai shekaru 17 da wata mata mai shekaru 23 a gagarumar zanga-zangar aka kaddamar a jiya Laraba. Sannan an hallaka wani soja a wajen Caracas, abin da ya kawo adadin mutanen da aka kashe yanzu zuwa 8.

‘Yan Sandan kwantar da tarzoma sun harba hayaki mai sa hawaye kan matasan da ke jifar su da duwatsu.

Zanga-zangar ta adawa da karancin abinci da bukatar a gudanar da zabe ta bazu daga Caracas babban birnin kasar zuwa sassan Venezuela.

Sannan akwai magoya bayan shugaba Nicolas Maduro da suka gudanar da zanga zangar nuna goyon baya ga shugaban da ya gaji Hugo Chavez.

Tun a 2014 Maduro ke fuskantar bore a Venezuela musamman kan adawa da tabarbarewar tattalin arzikin kasar mai dogaro da arikin fetir.

Faduwar farashin danyen mai ne ya haifar da tabarbarewar tattalin arzikin Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.