Isa ga babban shafi
Amurka-Korea ta Arewa

A shirye muke mu kai wa Amurka hari-Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta bayyana cewa a shirye take ta mayar da harin martani na makamin Nukiliya kan Amurka kamar yadda mutun na biyu mafi karfin fada a ji kasar ya sanar a wannan Asabar.

Korea ta Arewa ta gudanar da bikin nuna wa duniya karfin sojinta a wannan Asabar
Korea ta Arewa ta gudanar da bikin nuna wa duniya karfin sojinta a wannan Asabar REUTERS/Damir Sagolj
Talla

A jawabin da ya gabatar a wani kasaitaccen bikin nuna karfin sojin kasar a safiyar yau, Choe Ryong-Hae ya ce, za su rama duk wani harin makamin Nukiliya da aka kaddamar musu.

China da Rasha sun bukaci Koriya ta Arewa da Amurka da su kai zuciya nesa, yayin da ministan harkokin wajen China Wang Yi ya gargadi cewa, rikici ka iya barkewa kowanne lokaci tsakanin kasashen biyu.

Ana farbagar cewa, Korea ta Arewa za ta sake gwajin makamin Nukiliya a karo na shida duk da takunkuman da Majalisar Dinin Duniya ta kakaba ma ta saboda gwaje-gwajen da ta yi a baya.

Kazalika, kasar na da burin samar da rokan da zai isar da makami har zuwa tsakiyar Amurka, abin da shugaba Donald Trump ya ce, ba zai yiwu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.