Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Yaki na dab da barkewa tsakanin Koriya ta arewa da Amurka- China

China ta yi gargadin cewa yaki na dab da barkewa a kowane lokaci tsakanin koriya ta Arewa da Amurka a yayin da kasashen biyu ke wa juna barazana inda China ta yi kiran su kai zuciya nesa.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Ministan harakokin wajen China Wang Yi ne ya yi gargadin a lokacin da ya ke ganawa da takwaransa na Faransa Jean-Marc Ayrault da ya kai ziyara a Beijing

China ta ce yaki bai taba haifar da nasara ba, illa rungumar tattaunawar fahimtar juna.

Gargadin na China na na zuwa a yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai magance barazanar da Koriya ta Arewa ke yi wa kasar tare da shiga tsakanin China ko kuma Amurkan ta yi ta gaban kanta.

Sannan Trump ya ce yana nazarin daukar matakan soja akan Koriya ta arewa.

Barazanar Trump kuma na zuwa ne a daidai lokacin da Koriya ke shirin gudanar da bukukuwan cika shekaru 105 da haihuwar jagoran juyin juya halinta Kim Il-Sung, yayin da kuma rahotanni ke cewa kasar na shirin yin gwajin wani makami mai linzami a lokacin wannan biki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.