Korea ta Arewa ta ce hari da Amurka ta kai Syria shishshigi ne da babu yafiya
Kasar Korea ta Arewa ta soki kasar Amurka saboda hari da Dakarun Amurka suka kai Syria wanda Amurka ta ce ramuwar gayya ce saboda amfani da makamai masu guba da sojan Syria suka yi kan jama’a.
Wallafawa ranar:
Kalaman sun kasance irinsa na farko daga Korea ta Arewa tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci sojansa da su kai hari wani sansanin sojan Syria inda ake zaton daga nan ne aka cilla makamai masu guba da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 90.
Kamfanin Dillancin Labaran korea ta Arewa ya sanar da cewa Gwamnatin kasar na daukan harin da Amurka ta kai a matsayin ''shishshigi da ba za’a yafe ba''.
Saboda irin wannan katsalandan ne inji sanarwar ta sa Korea ta Arewa zama cikin shirin ko ta kwana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu