Isa ga babban shafi
Mexico-US

Mexico ta ce babu batun tursasa mata aiki da dokar hana baki na Amurka

Kasar Mexico ta lashi takobin hawa kujeran na ki gameda duk wani yunkuri da Amurka za ta yi na kakaba mata wasu sauye-sauye wajen harkan bakin haure.

Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto
Shugaban Mexico Enrique Pena Nieto REUTERS/Edgard Garrido
Talla

A yanzu haka dai Shugaban Mexico Enrique Pena Neito na ganawa da tawaga ta musamman na jami'an Gwamnatin Amurka bisa jagorancin Sakataren waje na Amurka Rex Tillerson, a birnin Mexico City.

Wannan ziyara dai na da zimmar ganin kasashen biyu sun dunke dukkan baraka tsakanin Mexico da Amurka.

Tun lokacin yakin neman zaben sa ne dai Donald Trump ke ikirarin zai yi aikin katangan, saboda yawanci manyan masu aikata laifuka ke tsallakawa zuwa Amurka.

Ministan waje na Mexico ya fadi cewa Gwamnatin Mexico da jama'a ba su yarda ba Gwamnatin wata kasa ta yi gaban kanta wajen gindaya doka da neman wata kasa ta bi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.