Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Ana bukatar dala biliyan 4 dan kaucewa yunwa a kasashe 4 - Guterres

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, yace Majalisar tana bukatar agajin gaggawa na Dala biliyan 4 da rabi dan magance matsalar yunwa a kasashe 4 da suka hada da Najeriya da Somalia da Sudan ta kudu da kuma Yemen.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Guterres yace mutane sama da miliyan 20 ke fuskantar barazanar yunwa a wadanan kasashe kuma ya zama wajibi a samun wadanan kudade nan da karshen watan gobe don kaucewa fuskantar sabon bala’i.

Sakataren yace ya zuwa yanzu, Majalisar ta samu Dala miliyan 90 daga cikin kudin, binda ke nuna akwai sauran kalubale muddin ba’a tashi tsaye ba.

Hukumar kula da kananan yara ta UNICEF tace akalla yara miliyan 1 da rabi ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki a wadannan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.