Assad ya bayyana Trump a matsayin aboki
Shugaban Syria Bashar al- Assad ya bayyana zababen shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin abokin tafiya muddin ya cika alkawarinsa na yaki da ta’addanci.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A hirarsa ta farko da aka watsa ta kafar talabijin tun bayan nasarar Trump, shugaba Assad ya ce, duk da ya ke yana da wahala a san abin da Trump zai yi, amma muddin ya sanya yaki da 'yan ta’adda a gaba, to a shirye suke su hada kai da shi kamar yadda kasashen Rasha da Iran suka yi.
Shugaban na Syria da kuma Rasha na ganin manufofin Amurka na yau na taimaka wa 'yan ta’adda don karbe iko a kasar, yayin da Amurka ke cewa, tana taimaka masu neman yanci ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu