Isa ga babban shafi
Rasha

Trump ya tattauna da Putin ta Tarho

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna da zababben shugaban Amurka Donald Trump inda suka amince da shirin daidaita dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu.

Zababben Shugaban Amurka Donald Trump
Zababben Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Fadar gwamnatin Rasha ta ce shugabannin biyu sun amince a shirya wata ganawa a tsakaninsu domin ci gaba da tuntubar juna.

Majiyoyi na kusa da Trump sun ce shugaban Rasha ne ya kira zababben shugaban domin taya shi murnar samun nasara a zaben shugaban kasa.

A cikin tattaunawar, shugabannin biyu sun amince su ta’addanci da tsatstsauran ra’ayi a duniya tare da tattauna batun magance rikicin Syria.

Kasashen biyu dai sun yi hannun riga ne a rikicin Syria inda Rasha ke goyon bayan gwamnatin Assad yayin da Amurka kuma ke mara wa ‘Yan tawaye baya. Amma ana ganin abubuwa za su iya sauyawa a zamanin Trump.

Wani na kusa da Donald Trump ya ce shugaban mai jiran gado ya tattauna da shugaban kasar China Xi Jingpin inda suka amince su bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kafin dai gudanar da zabe, Donald Trump ya yi ta barazanar sanyawa kayayyakin da ake yi a China haraji da kusan kashi 45 don ganin ya farfado da masana’antun Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.