Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton da Trump sun caccaki juna a muhawarar karshe

‘Yan takarar shugabancin Amurka guda biyu Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat sun sake fafatawa a muhawarar karshe kafin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Nuwamba.

Hillary Clinton da Donald Trump a muharar karshe da suka fafata a Las Vegas
Hillary Clinton da Donald Trump a muharar karshe da suka fafata a Las Vegas REUTERS/Mike Blake
Talla

‘Yan takarar biyu sun caccaki juna a muhawarar inda Donald Trump ya ki cewa ko zai amince da sakamakon zaben 8 ga watan Nuwamba idan har Hillary Clinton ce ta yi nasara.

Clinton ta ce kin amincewa da sakamakon zaben tamkar suka ne ga shekaru 240 na ci gaban dimokuradiyar Amurka.

Sannan ta danganta Trump a matsayin dan takara mafi hatsari da ya tsaya tarakar shugaban kasa a tarihin ci gaban siyasar Amurka.

‘Yan takarar guda biyu sun gudanar da zazzafar muharar ne akan batutuwa da dama da suka hada da batun ‘yancin zubar da ciki yayin da Hillary Clinton ke goyon baya, Donald Trump kuma ke adawa.

Wani babban batu shi ne batun shigar baki Amurka inda Donald Trump ke jaddada matakinsa na tsawwala tsaro akan iyakokin Amurka tare da karfafa mayar da baki kasashensu.

Clinton kuma ta yi bayani ne akan hanyoyin da za ta karbi bakin a Amurka.

‘Yan takarar sun yi musayar kalamu akan batun Rasha musamman fallasar da Wikileaks ya yi na bayanan sirrin Imel na Hillary Clinton.

Clinton ta yi zargin cewa Shugaban Rasha Vladimir Putin na goyon bayan yakin neman zaben Donald Trump.

Sannan ta ce wasu rahotannin sirri sun tabbatar da Rasha ta kutsa cikin shafin intanet na yakin neman zabenta.

Trump dai bai ce komi akan zargin alakar shi da gwamnatin Rasha. Amma ya ce zai fi inganta huldar Rasha da Amurka fiye da Clinton. Yana mai cewa Hillary ba ta da mutunci a idon Putin.

A yayin da ya rage saura kwanaki 20 a gudanar da zaben, Donald Trump ya so ya yi amfani da muhararar ta uku da aka gudanar a Las Vegas domin farfado da kwarjininsa a yakin neman zaben shi.

Yakin neman zaben Trump ya fuskanci koma baya musamman kan zarge-zargen da aka bankado na alakar shi da Mata, inda mata da dama suka fito suna zargin ya ci zarafinsu, wanda ya ce sharri ne da yarfen siyasa daga bangaren Clinton.

Trump ya yi zargin cewa akwai miliyoyan masu jefa kuri’a na jabu da aka yi wa rijistar zabe tare da cewa Hillary Clinton ba ta cancanci tsayawa takarar zaben shugaban kasa ba saboda barnar da ta aikata a lokacin da tana Sakatariyar harakokin wajen Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.