Isa ga babban shafi
Iraq

Sojin Iraqi na dab da kwato garin Kiristoci daga IS

Dakarun Iraqi da ke kokarin fatattakar mayakan IS a birnin Mosul, na dab da karbe garin Qaraqosh da ya kasance mafi girma ga mabiya addinin Kirista a kasar.

Sojojin Iraqi na ci gaba da yaki na nufin fatattakar mayakan IS a birnin Mosul na kasar
Sojojin Iraqi na ci gaba da yaki na nufin fatattakar mayakan IS a birnin Mosul na kasar REUTERS
Talla

Karbe wannan garin zai zama babbar nasara ga dakarun Iraqi a yakin da suke yi da nufin ‘yanto birnin Mosul daga hannun mayakan masu ikirarin jihadi.

Tuni dai mabiya addinin Kirista a Iraqi suka fara murna ta hanyar wake-wake da raye-raye har ma da kunna kyandir saboda kokarin dakarun kasar na kwato musu garin nasu.

Gabanin mayakan IS su kwace garin shekaru biyu da suka shude, Kiristoci fiye da dubu 50 ne tare da coci-cocinsu na Ibada ke rayuwa a garin

A jiya Talata ne dai, dakarun suka kutsa Qaraqosh mai tazarara kilomita 15 daga kudu maso gabashin Mosul, amma dai har yanzu mayakan IS na cikin garin.

A ranar Litinin da ta gabata ne, sojojin Iraqi suka fara kaddammar da farmakin kan mayakan na IS a Mosul wanda shi ne birnin na biyu mafi girma a kasar.

To sai dai wasu manyan kasashen duniya da suka hada da Amurka da Faransa sun gargadi cewa, da yiwuwar a shafe tsawon watanni a na dauki ba dadi mai zafi kafin sojojin su yi nasarar kawato Mosul daga hannun IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.