Dakarun Iraqi na ci gaba da kutsa kai Mosul
Yau ranar ta biyu dakarun Iraqi na sake nausa kai Mosul, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke sake bayyana furgaba game da makomar fararen hula sama da miliyan daya da rabi da ke rayuwa a birnin na Iraqi, a gaggarumin farmaki kwato yankin daga hannu mayakan IS.
Wallafawa ranar:
Wani babban jami’in Majalisar ya yi gargadi samun Karin miliyoyin ‘yan gudun hijira sakamakon wannan farmaki.
A cewar Jami’in, Lise Grande, kamar yadda suka samu bayanai nan da kwanaki 5 zuwa 6 za a samu daruruwan ‘yan gudun hijira da ke neman tsira daga Mosul.
Tun a shekarar 2014 IS ke iko da Mosul, sai dai dakarun na Iraqi da taimakon rundunar kawance Amurka, na samun gallaba kan mayakan a hare hare sama da ake kai wa cikin garin.
Shugaban kasar Turkiya, Recep tayyib Erdogan, ya ce kasarsa za ta bayar da gudunmawa a yakin, inda ya ce wanann yaki ba wanda Ankara za ta zura ido ba ne.
Kungiyar IS da ke kokarin kafa daularta a Syria da Iraqi na fusknatar koma baya a ayyukan ta na jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu