Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya kaucewa biyan wani bangare na harajinsa shekaru 18

Wasu bayanai da jaridar The New York Times ta wallafa na nuni da cewa dan takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Republican Donald Trump, ya bayyana cewa ya yi asara ta sama da dala bilyan daya a shekarar 1995, abin da ya sa aka yi masa sassaucin biyan haraji a cikin shekaru 18 da suka biyo baya.

Dan takarar Republican Donald Trump.
Dan takarar Republican Donald Trump. REUTERS/Mike Segar
Talla

Bayanan da jaridar ta wallafa sun zo ne a daidai lokacin da Donald Trump ke ci gaba da shan matsin lamba domin ya wallafa takardunsa na biyan haraji, abin da kuma ya ki.

Ana zargin cewa dan takarar na Republican a zaben watan nuwamba mai zuwa, ya kaucewa biyan harajin wasu kamfanoninsa da suka hada da na caca, da jiragen sama da kuma otel-otel.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.