Isa ga babban shafi
Brazil

An tsige Rousseff a Brazil

Majalisar Dattijai a Brazil ta tsige shugabar kasar Dilma Rousseff bayan kada kuri’ar da ta kawo karshen mulkin jam’iyyarta na shekaru 13. Rousseff ta danganta matakin a matsayin juyin mulki.

Brazilian President Dilma Rousseff
Brazilian President Dilma Rousseff REUTERS
Talla

‘Yan majalisa dattijai 61 ne cikin 81 suka kada kuri’ar amincewa da tsige Dilma Rousseff mai shekaru 68.

Kuma dama idan kashi biyu cikin uku suka amince to babu shakka Rousseff ta tsigu.

An tsige Rousseff ne akan laifin badakalar coge a kasafin kudin kasar.

Sai dai yunkurin haramta ma ta rike wani mukamin siyasa bai cim ma nasara ba a zauren majalisar, wanda hakan ke nuna za ta iya dawo wa fagen siyasa.

Babu dai wani lokaci da aka tsayar da za ta fice daga fadar shugaban kasa.

A lokacin da ta ke mayar da martani Dilma Rousseff ta danganta matakin na tsige ta a matsayin juyin mulki, tana mai cewa an zartar da hukunci akan marar laifi.

Rashin dai haramta ma ta rike wani mukamin siyasa, na iya sa ta dawo a dama da ita.

Yanzu mataimakinta Michel Temer ne shugaban kasa na rikon kwarya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.