Isa ga babban shafi
North Korea

Koriya ta Arewa ta ce Jakandan ta da ya tsere mai laifi ne

Kasar Koriya ta Arewa ta ce Jakadanta da ya tsere zuwa Koriya ta kudu mai laifi ne wanda aka umurce shi da ya koma gida don ya amsa tanbayoyi.

Hoton Jakada Thae Yong-Ho
Hoton Jakada Thae Yong-Ho Reuters
Talla

Jakada Thae Yong-Ho cikin wannan mako mai karewa ya tsere zuwa kasar Koriya ta Kudu a wani lokaci da dangantaka tsakanin kasashen biyu ke tsami.

Kamfanin Dillancin labaran kasar Koriya ta Arewa ya fadi cewa  ana zargin jakadan ne da sace kudaden Gwamnati, da yin fyade da kuma yiwa Koriya ta Kudu aikin leken asiri yana samun kudade.

 

 

 

Shi dai Jakada Thae na aikin sa ne a Britania kafin ya shiga cikin wannan hali.

Koriya ta Arewa ta zargi Britaniya da kin mika mata shi wannan jakada aka mika shi zuwa ga Koriya ta kudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.