Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta samu goyon bayan mallakar nukiliya

Taron Jam’iyyar da ke mulki a Koriya ta Arewa na farko a cikin shekaru 40, ya goyi bayan shirin shugaba Kim Jong-Un na kara yawan makaman nukiliyar kasar.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un Reuters
Talla

Ana ganin taron wanda aka bude ranar juma’ar da ta gabata, a matsayin bikin karrama shugaban kasar mai shekaru 33 Kim Jong-Un a matsayin shugaban kasa mai karfin fada aji da kuma mallakar makamin nukiliya.

Jiya L ahadi mahalarta taron sun amince da rahotan da shugaban ya gabatar mu su na bunkasa tattalin arziki da kuma fadada gina makaman nukiliya domin kare kasar.

Rahotan ya kunshi sharadin cewar, ba za ayi amfani da makamin nukiliyar ba har sai an yi wa kasar ta su barazana, wato duk wanda ya ce wa kasar kule su kuma za su ce cas.

Rahotan ya kuma kunshi shirin hadewar mashigin ruwan Koriya da sharadin cewar, idan Koriya ta kudu ta bukaci a fafata yaki, toh za su share ma su kiyayya da shirin daga doron kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.